Gwamnatin Tarayya ta ware jumillar kudi naira Miliyan dubu 863 domin shirye-shiryenta daban-daban na tallafi

0 199

Gwamnatin Tarayya ta ware jumillar kudi naira Miliyan dubu 863 domin shirye-shiryenta daban-daban na tallafi domin shekara mai zuwa wacce za ta ‘kare a watan Disambar 2022, adadin da ya kai kashi 5.3 cikin 100 na jumillar kudaden kasafin kudin naira tiriliyan 16 da Miliyan dubu 390.

Shirye-shiryen tallafin na musamman sun hada da shirin rage fatara da talauci da ya kunshi kara kudaden shirye-shiryen tallafawa jama’a.

Kididdigar alkaluman ya nuna cewa a karkashin kudaden da aka ware, gwamnatin tarayya tayi niyyar kashe naira Miliyan dubu 410 a shirinta na rage fatara da talauci.

Kazalika, akwai karin naira Miliyan dubu 300 da aka ware a matsayin kason gwamnatin tarayya na shirin rage fatara da talauci da samar da cigaba na kasa.

Ana sa ran shirye-shirye na musamman zasu lakume kudi naira miliyan dubu 60 da miliyan 920, yayin da ma’aikatar harkokin jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a zata samu naira miliyan dubu 62 da miliyan 590, inda ma’aikatar harkokin mata ake sa ran za ta samu naira miliyan dubu 8 da miliyan 50.

Leave a Reply

%d bloggers like this: