Gwamnatin Tarayya ta wanke mutane 888 daga zargin ta’addanci

0 46

Gwamnatin Tarayya ta bayyana wanke mutane 888 da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci, bayan rashin isassun hujjoji da ke tabbatar da laifin da ake zarginsu da shi, duk da tsawon shekarun da suka shafe a hannun hukuma.

A zaman shari’ar da cibiyar yaƙi da ta’addanci ta kasa, ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, an yanke hukunci kan waɗanda ake zargi da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram da wasu ƙungiyoyin ta’addanci.

Rahotanni sun nuna cewa mutane dubu 1,743 ne suka gurfana a zaman shari’ar, inda aka kasa su zuwa rukuni shida.

Daga cikinsu, mutane 200 an tabbatar da alaƙarsu da ayyukan ta’addanci, yayin da aka wanke mutane 888 saboda rashin hujjoji, sai kuma wasu 92 da aka ɗage shari’arsu.

Tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu, kotu ta yanke wa mutane 742 hukunci, yayin da aka ci gaba da shari’ar wasu.  Wannan mataki ya nuna cewa har yanzu akwai ƙalubale wajen tabbatar da adalci a sha’anin yaƙi da ta’addanci a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: