Gwamnatin tarayya ta umarci a kwashe manyan motocin da suke kan hanyar Abuja-Kaduna zuwa Kano
Gwamnatin tarayya ta umarci a kwashe manyan Motocin da suke kan hanyar Abuja-Kaduna zuwa Kano kafin karshen shekarar da muke ciki.
Gwamnatin ta ce taruwar motocin akan hanyar yana haifar da tsaiko akan hanyar musamman ga Matafiya.
Daraktan Gina Manyan Hanyoyin da Gyara su na Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, wanda kuma shine Shugaban Kwamatin Kula da Manyan Hanyoyi Injiniya Folorunsho Esan, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake ziyartar hanyar.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta kafa Kwamatin kula da ayyukan hanyoyin gwamnati.
Injiniya Esan, ya ce Ma’aikatar zata samar da wurin Ajiye motoci na wucin gadi wanda yake Tafa, akan hanyar Kaduna, ta yadda kimanin Motoci 500 zasu rika tsayawa, domin magance matsalolin tsayawa akan hanyar.