‘Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf domin harba karin tauraron dan’adam guda 2 a Najeriya’
Gwamnatin Tarayya a jiya tace ta shirya tsaf domin harba karin tauraron dan’adam guda 2 daga hukumar kula da tauraron dan’adam ta kasa.
Ministan sadarwa da tattalin arziki, Farfesa Isa Ali Pantami, ya sanar da haka yayin rangadin kayan aikin hukumar tare da ganawa da shugabannin hukumar a Abuja.
Isa Pantami ya kuma ce muddin hukumar na gudun sake sayar da ita ga ‘yan kasuwa, dole ne take samar da ayyuka masu inganci tare da tara kudaden shiga masu yawa.
Ministan ya kuma ce manufar ziyarar tasa ita ce magance manyan matsalolin dake bukatar kulawa daga gwamnatin tarayya.
Darakta-Janar ta hukumar, Abimbola Alale, ta yabawa yunkurin gwamnatin tarayya na tabbatar da cewa hukumar tana gudanar da ayyukanta kamar yadda ya kamata.