Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewar ta shirya tsaf domin bayar da cikakkiyar dama ga matatar man fetur ta Dangote wadda zata na tace gangar danyen mai dubu 650 a duk rana.
Gwamnatin ta sanar da haka ne a jiya a wajen zaman masu ruwa da tsaki kan harkokin manfetur da aka gabatar a Abuja.
Hukumar Kula da Harkokin Manfetur ta NMDPRA da ta shirya taron ta ce, tun a baya ta bayar da lasisin samar da matatar ta Dangote wadda aka samar da ita a kan kudi dala biliyan 20, kuma sannan nan ba da jimawa ba zata bayar da cikakken lasisin fara aiki ga matatar.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da matatar a watan Mayun bara, kuma a watan Aprilun da ya gabata ne matatar ta fara fitar da dizel ga kasuwannin Najeriya.