Gwamnatin tarayya ta raba Naira Biliyan 24 ga Jihohin Ebonyi da Yobe da Katsina

0 198

Gwamnatin tarayya ta raba Naira Biliyan 24 ga Jihohin Ebonyi da Yobe da Katsina da kuma babban birnin tarayya Abuja domin fara aiwatar da wurin kiwo na zamani.

Babban Mai Magana da yawun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Malam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan ta cikin shirin Politics Today na gidan Talabijin na Channels Tv.

A cewarsa, Jihohin 4 kowacce ta karbi Naira Biliyan 6 domin fara aiwatar da shirin da sauran abubuwa da shirin yake bukata.

Sai dai bai bayyana yau shene kudaden suka isa Jihohin ba, amma ya ce Jihar Katsina ce ta karshe da aka bawa kudin a kwanan nan.

Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya zata kara bawa wasu Jihohi 8 kudaden nan da kwanaki masu zuwa da zarar sun kammala shirye-shiryen da ake bukata.

Malam Garba Shehu, ya ce duk jihar da take bukatar samun kudaden, yana da kyau ta cika dukkan ka’idojin da ake bukata.

A cewarsa, kawo yanzu kimanin Naira biliyan 24 gwamnatin tarayya ta raba a Jihohin 4 ciki harda Abuja domin fara aiwatar da shirin.

Kazalika, ya ce shirin yana daya daga cikin hanyoyin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take dauka domin rage rikicin Manoma da Makiyaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: