Gwamnatin tarayya ta maka shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a gaban kotu

0 219

Gwamnatin tarayya ta maka shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, a gaban kotu kan laifukan da suka shafi ta’addanci.

Bodejo dai yana hannun hukumar leken asiri ta tsaro tun bayan kama shi a ranar 23 ga watan Janairu.

An kama shugaban kungiyar Miyetti Allah ne a jihar Nasarawa kwanaki bayan kungiyar ta kaddamar da kungiyar ‘yan banga mai suna Kungiyar Zaman Lafiya.

A wajen kaddamar kungiyar da ta kunshi Fulani 1,144 a ranar 17 ga watan Junairu, 2024, Bodejo ya ce an dauki matakin ne domin magance matsalar ‘yan fashi, satar shanu da duk wani nau’in rashin tsaro a jihar Nasarawa. Bayan kama shi, shugaban na Miyetti Allah ya shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja domin kalubalantar tsare shi da aka dade ana yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: