Ana bayyana hakan ne yayin da masu ruwa da tsaki a sassan sassan kasar nan suka hallara a jihar Ekiti domin halartar taron majalisar kula da lafiya na kasa karo na 64 inda ake tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi harkar lafiya.
Bikin bude taron a jiya mai taken mayar da hankali kan gina tsarin kiwon lafiya da ya hada da inganta hakokin kiwon lafiya a Najeriya.
Ministan lafiya da walwalar jama’a Dr Muhammed Ali Pate ya ce cibiyoyin kiwon lafiyar kasar nan suna cikin mummunan hali, yana mai cewa akwai bukatar a dauki matakin gaggawa.
A watan da ya gabata ne Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-baci a fannin kiown lafiya tare da warewa bangaren makudan kudade a cikin kasafin kudin 2024. Kiran dai ya biyo bayan kudirin da wani dan majalisa daga jihar Legas, Fayinka Oluwatoyin na jam’iyyar APC ya gabatar a yayin zaman majalisar da aka yi a Abuja.