Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na dakile tashin gouran zabin farashin magunguna

0 209

Yayin da yan najeriya ke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki, Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na dakile tashin gouran zabin farashin magunguna a fadin kasar ta hanyar karfafa masana’antun magunguna na cikin gida.

Ministan lafiya da walwalar jama’a Farfesa Ali Pate ne ya bayyana hakan jiya a Legas yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar harhada magunguna.

Ya ce yayin da hauhawar farashin magunguna ya zama ruwan dare a duniya, gwamnatin shugaba Bola Tinubu na daukar matakan tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun samu kayayyaki masu sauki don inganta kiwon lafiyar su. Shugaban kungiyar hadin kan masana’antun harhada magunguna ta kasa, Dakta Okey Akpa a madadin masu ruwa da tsaki, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da asusu na bunkasa masana’antar harhada magunguna na Naira biliyan 600 a babban bankin kasa (CBN) ko kuma bankin masana’antu. Domin bunkasa samar da magunguna da alluran rigakafi, da kayayyakin aiki, da kuma Bincike da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: