Gwamnatin tarayya ta hana fitar da gas ɗin girki zuwa ƙasashen waje

0 44

Daga ranar 1 ga watan Nuwamba mai kamawa, Gwamnatin tarayya za ta hana fitar da gas ɗin girki zuwa ƙasashen waje a wani mataki da ta ce ta ɗauka domin hana hauhawara farashin gas.

Ƙaramin ministan albarkatun mai, mai kula da harkokin gas, Ekperikpe Ekpo, ne ya bayyana haka, a cikin irin matakan da ya ce gwamnati ta ɗauka domin tabbatar da saukinsa.

Ministan ya nuna damuwarsa kan yadda farashin gas ɗin ke ta hauhawa a baya-bayan nan daga tsakanin naira 1,100 da 1,250 zuwa naira 1,500 a kan kilo ɗaya.

A kan hakan ministan ya yi taro da masu ruwa da tsaki a kan gas a jiya Talata Abuja, domin lalubo hanyoyin magance matsalar hauhawara farashin, wadda ke damun ‘yan ƙasar.

A nan ne ministan ya sanar da cewa daga cikin muhimman matakan da aka ɗauka sun haɗa da umartar kamfanin mai na ƙasar NNPCL da masu samar da gas ɗin na cikin ƙasa da su daina fitar da gas ɗin da aka samar a ƙasar zuwa waje. A wata sanarwa da kakakin ministan, Louis Ibah, ya fitar ya ce an bai wa hukumomin da ke aikin hakowa da sayar da albarkatun mai na ƙasar da su fitar da wani tartibin tsarin farashin gas ɗin na cikin gida nan da kawanaki 90 watanni 3 kenan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: