Gwamnatin tarayya ta dakatar da ayyukan kamfanin sifurin jirgin samanta na Air Nigeria

0 243

Gwamnatin tarayya ta dakatar da ayyukan kamfanin sifurin jirgin samanta na Air Nigeria, har sai Baba ta gani.

Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo, ne ya sanar da hakan yayin taron Ministoci na cikar shekarar Tinubu, guda a kan mulkin kasar.

Ya ce, matakin ya zo ne, lura da cewa kamfanin a ko da yaushe yunkurin yin amfani da jiragen saman wasu kasashen waje ya ke a matsayin na ta.

Idan za a iya tunawa, a shekarar 2023 ne, ma’aikatar sufurin jiragen sama, karkashin jagorancin tsohon ministan sifuri Sanata Hadi Sirika, ta kaddamar da kamfanin jirgin mallakin Najeriya, wato Nigerian Air kwanaki uku kafin karshen wa’adin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lamarin dai ya yanwo cece-kuce a tsakanin al’ummar kasa, la’akari da yadda daga bisani aka gane cewa akwai kuskunda a cikin batun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: