Gwamnatin Tarayya ta cewa ba ta cikin mafi kyawun matsayin sarrafa matatun man kasar.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, shine ya bayyana hakan a jiya Alhamis.
Ya yi bayanin cewa gwamnati ba ta yarda da ra’ayin sayar da matatun mai a halin da suke ciki saboda irin wannan matakin zai sa suka daga ‘yan kasa.
Ya kara da cewa ba za a zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da halin da cibiyoyin ke ciki ba saboda ta gaji matatun mai da suka lalace.
Duk da wannan, ya ce gwamnati ta yanke shawarar tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa za a iya gyara matatun sannan a mayar da su cikin yanayin aiki. Bayan an gyara matatun man, ministan yace za’a tabbatarwa yan kasa yadda za’a gudanar dasu.