Gwamnatin Tarayya ta bayar da tabbacin cewa tana kokarin shawo kan matsalar karancin abinci kuma nan ba da jimawa ba farashin kayan masarufi zai sauko.
Alkaluman baya-bayan nan daga rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS), sun nuna cewa hauhawar farashi ta zarta kaso 40 cikin 100 a ‘yan watannin baya, abin da ya sanya farashin kayan masarufi ya fi karfin miliyoyin mutane.
Sai dai karamin ninistan aikin gona, Aliyu Abdullahi, ya ce dimbin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta bijiro da su, za su sassauta farashin kayan masarufin.
Ya bayyana haka ne cikin wani shiri na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
“Za a ga dimbin tsare-tsaren da aka bijiro da su domin sassauta yanayin.
A cewar Abdullahi, “harkar noma abu ne da yake da lokaci. A halin yanzu, ana ta aikin gona. A cikin damina muke kuma idan ka kalli gonaki, za ka ga ana ta aikin noma. Shuke-shuken ba su zamo abinci
Ministan ya ce a baya kasar nan ta dogara ne a kan noman damina.
Sai dai ya sanar da cewa ma’aikatarsa na kokarin shawo kan matsalar, inda ya ce “sun gano cewar tsawon shekaru ba,a daukar noman rani da muhimmanci.”