Gwamnatin tarayya ta ce ba ta duba yiwuwar kakaba dokar kulle ba duk da karuwar adadin masu harbuwa da cutar Corona
Gwamnatin tarayya ta ce ba ta duba yiwuwar kakaba dokar kulle a kowane bangare na kasarnan duk da karuwar adadin masu harbuwa da cutar corona.
Ministan kiwon lafiya, Dr Osagie Ehanire, wanda ya zanta da manema labarai jiya a Abuja, ya ce za a iya kakaba dokar kulle ne kawai a matsayin mataki na karshe saboda dokar na dakile ayyukan tattalin arziki da tauye ‘yancin bil’adama da takaita harkokin kasuwanci.
Gwamnatin tarayya ta kakaba dokar kulle a kasa baki daya na wasu makonni a bara a farkon zuwan corona amma ministan ya ce gwamnati ta koyi darussa daga wannan dokar kullen.
A halin yanzu Najeriya na fuskantar zagaye na uku na guguwar corona, lamarin da yasa ake samun karuwar masu kamuwa.
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa, NCDC, ta ce mutane 753 suka sake kamuwa da cutar ta korona jiya a fadin kasarnan.