Gwamnatin tarayya ta bukaci jama’a da su kauracewa shan ababen sha na gida domin kare kai da kamuwa da cutar kwalara

0 111

Karamin Ministan muhalli Iziaq Sala

Yayin da alkaluman masu kamuwa da cutar amai da gudawa ta kwalara ke karuwa a kasa, gwamnatin tarayya ta bukaci yan kasa da su kauracewa shan ababen sha na gida kamar kunu, zobo da fura domin kare kai da kamuwa da cutar.

Karamin Ministan muhalli Iziaq Salako ne ya bayar da wannan shawarar cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Salako ya bukaci yan kasa da su dauki kwararan matakan kare kai da suka hada da tsaftace muhalli da kula magudanan ruwa yadda ya kamata.

Kazalika ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi dana kananan hakumomi da su fadada ayyukan wayar da kai kan muhallai da kayayyakin abin ci da na sha na sayarwa a fadin kasa.

Salako yayi amannar cewa daukar matakan da suka kamata zai taimaka wajen rage kamuwa da yaduwar cutar a cikin jama’a.

Ya kuma yi kira ga dukkan kwamshinonin muhalli da shugabannin kananan hakumomi su tallafawa ma’aikatan tsaftar muhalli wajen samar da kayayyakin aiki domin tabbatar da kare muhalli daga daukar cutukan daka iya kaiwa ga Bazuwa cikin jama’a.          

Leave a Reply

%d bloggers like this: