Gwamnatin tarayya ta bukaci hadin kan shugabannin Arewa domin dakile matsalar tsaro

0 326

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci shugabannin arewa da su marawa kokarin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu baya domin dakile matsalolin tsaro.

Shettima yayi wannan kira ne a Sokoto lokacin da ya kai ziyarar barka da sallah ga mai alfarma sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III a fadar sa da ke Sokoto.

Yayin da yake mika sakon shugaban kasa na barka da sallah mataimakin shugaban kasar ya jaddada muhimmancin zaman lafiya, da hadin kai, yayin da yake cewa baza’a taba samun zaman lafiya ba tare da cigaba ba, kamar yadda baza’a zamu cigaba ba tare da zaman lafiya ba.

Yace gwamati mai ci tana matukar mutunta masarautun gargajiya, kuma zata ci gaba da bada dukkan goyon bayan da ya kamata domin cigaban kasa. Kazalika mataimakin shugaban kasar ya kuma bukaci gwamnan jihar Dr Ahmed Aliyu Sokoto da yayi aiki da dukkan masu ruwa tsaki a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: