Gwamnatin tarayya ta bakin ma’aikatar bunkasa ma’adanai ta kasa, ta bayyana shirinta na sake duba farashin lasisin hakar ma’adanai da sauran kudaden da masu aikin hakar ma’adanai ke biya a kasar nan.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman ga karamin ministan ma’adanai na kasa Segun Tomori.
Da yake jawabi yayin wani taron tuntuba na masu ruwa da tsaki a jiya Alhamis a Abuja, Ministan ya bayyana cewa shirin zai inganta kudurin gwamnati na sake farfado da bangaren ma’adinai yadda ya kamata.
Ya jaddada cewa sake duba farashin ya zama wajibi idan har gwamnati za ta dauki nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da yanayi mai kyau ga ayyukan hakar ma’adinai tare da kara samun kudaden shiga.
Ministan ya nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki kan karin kudin lasisin hakar ma’adinai da sauran kudaden da suke da kudurin yin karin su a nan gaba.