Gwamnatin Tarayya ta bayyana kudirin ta na inganta fannin noma da samar da abinci a kasar nan

0 247

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana haka jiya a wurin taron fadada harkokin noma a Afrika karo 6 wanda ya gudana a Abuja.

Shugaban wanda ya samu wakilcin karamin Ministan Noma da samar da abinci Sanata Aliyu Abdullahi.

Shugaban kasa Bola Tinubu yace gwamnatin tarayya ta sanar amfanin noma da samar da abinci wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.

Ya ce za’a shigo da kwararru cikin harkokin Noman kasar nan, tare da samar da kayan aikin gona na zamani ciki hadda takin zamani da kayan noman rani a farashi mai rahusa domin samun wadataccen abinci.

Shugaba Tinubu yace fadada aikin noma na bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban cibiyar bunkasa cibiyar fasahar bincike ta aikin gona a kasar nan. A nasa jawabin, babban sakataran ma’aikatar aikin Gona Dakta Ernest Umakhihe, yace fadada aikin gonda yana da amfanin da baza’a iya misaltawa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: