Gwamnatin tarayya ta bayyana buƙatar gaggawa ta ganin Cibiyar murƙushe ta’addanci a Afirka

0 177

Gwamnatin tarayya ta bayyana buƙatar gaggawa ta ganin Cibiyar murƙushe ta’addanci a Afirka ta kama aiki gadan-gadan a ƙoƙarin dukkan masu ruwa da tsaki a nahiyar na kawar da ta’addanci.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce lallai bai kamata ƙasashen Afirka su yi biris da tunanin kafa wata rundunar ko-ta-kwana a nahiyar ba, wadda ayyukanta za su haɗar da tunkarar ta’addanci.

Ya bayyana haka ne yayin buɗe wani babban taron wuni biyu don ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe Afirka da bunƙasa cibiyoyin gwamnati, don shawo kan matsalolin ta’addanci.

Kasashen Afirka dai musamman na yammaci na fama da matsalar tsaro da ke haddasa rasa dubban rayuka da tilasta miliyoyi barin muhallansu. Masana fannin tsaro na yi wa taron na Abuja kallon wani ɗan-ba da za a dasa wanda ka iya samar da bakin zare ga matsalar da ke ci wa yankin tuwo a kwarya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: