Gwamnatin Tarayya ta baiwa Jihar Jigawa taki na ruwa lita 155,000 domin rabawa manoma

0 188

Gwamnatin jihar Jigawa ta karbi karashen kason taki na ruwa lita dubu dari da hamsin da biyar daga gwamnatin tarayya domin rabawa ga manoman da suka gamu da iftila’in ambaliyar a shekarar 2018.

Mataimakin Gwamnan jiha Injiniya Aminu Usman Gumel ne ya bayyana haka a lokacin da yake karbar takin daga hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA.

Yace za’a yi adalci wajen rabon takin ga al’ummomin da suka gamu da iftila’in ambaliyar a kananan hukumomin Kafin Hausa da Auyo da kuma Miga.

Daga nan mataimakin gwamnan, amadadin Gwamnati da al’ummar jihar Jigawa, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma babbar Daraktar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa bisa bada tallafin A jawabinta, Babbar Daraktar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA Hajiya Zubaida Umar wanda Daraktan kudi na hukumar Malam Sani Jiba ya wakilta, tace takin wani kaso ne na karashen takin da aka bayar ga wadanda suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a shekarar 2018.

Leave a Reply

%d bloggers like this: