Gwamnatin Tarayya ta bai wa NLC da NANS kyautar motoci 64 masu amfani da gas

0 110

Gwamnatin Tarayya bai wa Ƙungiyoyin Ƙwadago na NLC da TUC da Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS), kyautar motoci masu amfani da iskar gas (CNG), domin sauƙaƙa harkar sufuri.

Ministan Kuɗi, Wale Edun ne, ya jagoranci tawagar gwamnati wajen raba motocin wanda ya ce yana daga cikin alƙawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na samar da ingantaccen sufuri mai sauƙi ga ‘yan Najeriya bayan cire tallafin man fetur.

Edun, ya bayyana cewa manufar shirin shi ne rage wa talakawa da mabuƙata wahala da kuma tallafa wa gyaran tattalin arziƙin ƙasa don ɗorewar tattalin arziƙin Najeriya.

Ya ƙara da cewa bayar sa motocin 64 yana nuna farkon ƙaddamar da wani babban mataki, inda ake shirin raba motoci sama da 500 masu amfani da iskar gas da motoci masu amfani da lantarki guda 100.

Ya ƙara da cewa wannan shiri yana da alaƙa da yunƙurin Najeriya na amfani da makamashi mai tsafta tare da yin amfani da albarkatun makamashin ƙasa don bunƙasa masana’antu.

Ministan ya ce wannan tsari zai sauƙaƙa wa ma’aikata hanyar samun sufuri mai arha duba da yanayin hauhawar farashi.

Ya kuma bayyana cewa amfani da iskar gas yana da rahusa sosai, inda za a iya cika wa mutum abun hawa a kan Naira 15,000 kacal, maimakon sama da Naira 50,000 a man fetur.

Shugaban Shirin PCNGi, Michael Oluwagbemi, ya ce tun lokacin da aka kafa shirin shekara guda da ta gabata, an kafa cibiyoyi 125 don sauya motoci zuwa CNG, inda aka gina manyan gidajen sayar sa iskar gas 12, kuma ana kan gina wasu 75.

Ya ce ana canza motoci daga tsarin amfani da man fetur zuwa iskar gas a jihohi takwas, kuma za a faɗaɗa shirin zuwa jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

Shugabannin TUC, NLC, da NANS sun yaba wa gwamnatin kan ba su kyautar motocin.

Sakataren TUC, Kwamared Nuhu Toro, ya gode wa Shugaba Tinubu saboda amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.

Ya bayyana cewa wannan babban mataki ne da zai rage wa ma’aikata nauyin wahalhalun tattalin arziƙi.

A nasa ɓangaren, shugaban NANS, Kwamared Lucky Emonefe, ya jinjina wa gwamnati saboda jajircewarta game da harkar ilimi da jin daɗin dalibai.

  • Aminiya

Leave a Reply

%d bloggers like this: