Gwamnatin Tarayya ta amince da gina wa alkalai gidaje 40 a Abuja

0 110

Gwamnatin Tarayya ta amince da gina wa alkalai gidaje 40 a Abuja cikin shirin “Renewed Hope Agenda”. 

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ne, ya sanar da wannan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da Shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a jiya Litinin.

An tsara gina gidajen ne don samar da wuraren zama masu aminci ga ma’aikatan shari’a, inda aka ware gidaje 20 ga Babbar Kotun Abuja, gidaje 10 ga Babbar Kotun Tarayya, da gidaje 10 ga Kotun Daukaka Kara, duk a unguwar Kantampe.

Wike, ya bayyana cewa aikin za a kammala shi cikin watanni 15, wanda zai magance matsalar alkalai na zaman gidajen haya da otal-otal.

Haka kuma, an amince da wasu ayyukan gine-gine a kauyukan Abuja, inda za a samar da hanyoyi masu tsawon kilomita 75 a Kwali, Gwagwalada, da Bwari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: