Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago NLC basu cimma matsaya ba kan kudirin shiga yajin aiki

0 289

Zaman tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago NLC ta kare ba tare da an cimma matsaya ba, dangane da bukatun kungiyar.

Ministan kwadago Simon Lalong da kuma karamin Ministan kwadago Nkeiruka onyejeocha, sun gana da shugaban kungiyar na kasa Joe Ajaero da sauran shugabannin kungiyar a Abuja, a kokarin shawo kan kungiyar bisa kudirin ta na shiga yajin aikin gama gari.

Amma dai ana tsammanin za’a cigaba da zaman a wata rana ta daban.

Kazalika, Ministan kwadagon ana tsammanin zai yi wani zaman da kungiyar kwadago ta masu masana’antu TUC a yau.

Zaman na su, ya biyo bayan gayyatar Ministan kwado domin ganawa da shugabannin kungiyar domin shawo kan su a kokarin yajin aikin da suke shirin shiga biyo bayan janye tallafin man fetur.

Tunda farko,Ministan kwadado ya gayyaci kungiyoyin kwadago na NLC da kuma TUC, domin tattaunawa da su kan yajin aikin da suka yi a ranakun 5 da 6 na wannan wata.

Yayin zaman na su na jiya, Ministan kwadado yayi alkawarin zai hada kai da kungiyar kwadagon domin biya musu bukatun su. Ya kuma bukaci kungiyar da su kasance masu gaskiya akan dukkanin abunda su tattauna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: