Gwamnatin shugaba Buhari ta yiwa Ma’aikatar Harkokin Neja-Delta binciken kwakwaf

0 153

Ma’aikatar Harkokin Neja-Delta ta gabatar da rahoton da aka jima ana jira na binciken kwakwaf a hukumar raya yankin Neja Delta ga gwamnatin tarayya.

Da yake gabatar da rahoton yau ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hannun Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Ministan Harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya ce binciken da aka gudanar ya gano kimanin ayyuka dubu 13 da 700 da aka yi watsi da su.

Ya kuma bayyana cewa an tura jami’ai kimanin 390 da suka hada da sojoji, da ‘yan sanda, da ‘yan civil defence a cikin binciken.

Da yake jawabi, babban mai binciken, Alhaji Kabir Ahmed ya ce masu binciken kudi 16 ne suka gudanar da aikin na watanni 16.

A nasa jawabin, Abubakar Malami ya ce shugaban kasa ne ya kafa kwamitin binciken ne domin tabbatar da bin diddigin kusan naira tiriliyan 6 da aka fitar a matsayin kasafin kudin yankin Neja Delta tun daga lokacin da aka kafa hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: