Gwamnatin tarayya ta yi watsi da iƙirarin da jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, wanda ya shafe wata takwas yana tsare a ƙasar, kan zarge-zargen rashawa.
A kwanakin baya ne aka gurfanar da Gambaryan- ɗan Amurka – a kotun Najeriya bisa zargin laifukan kuɗi.
To sai dai hukumomin Najeriya sun sake shi ne bayan shiga tsakani da gwamnatin Amurka ta yi.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Gambaryan ya yi ikirarin cewa kama shi da gwamnatin Najeriya ta yi ba bisa ƙa’ida ba ya sa tsohon shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya kauce wa ganawar da ya shirya yi da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a yayin taron Majalisar Dinkin Duniya na 2024 (UNGA).
Ya kuma zargi mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu kan lamarin, sannan ya ce gwamnatin Amurka ta rage yawan wakilan Najeriya da suka halarci taron na MDD.
Jami’in na Binance ya kuma zargi wasu ƴan majalisar ƙasar uku da neman cin hancin dala miliyan 150 daga wajensa.
To sai dai a martanin da gwamnatin ƙasar ta mayar masa, ta ce zarge-zargen nasa ba su da tushe balle makama.
Cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya fitar, ya bayyana iƙirarin Gambaryan a matsayin tsantsar ƙarya da gangan.
“Gwamnatin Najeriya ta damu matuƙa da zarge-zargen marasa tushe, da kuma kalaman ɓatanci da Tigran Gambaryan, da aka yi wa shari’a a Najeriya kwannan kan laifukan kuɗi,” a cewar sanarwar.
Ta kuma ƙara da cewa ”gwamnati ta ki amincewa da tayin da Binance ta yi na biyan dala miliyan biyar don sakin Mista Gambaryan, don yin sulhu da gwamnatin Amurka.”
A farkon shekarar da ta gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta tsare Mista Gambaryan tare da abokin aikinsa, Nadeem Anjarwalla ɗan Kenya asalin Birtaniya mai shekara 37 bisa zargin laifukan ɓarnatar da kuɗi da hukumar EFCC ke bincike.
To amma a watan Maris ɗin shekarar Anjarwalla ya gudu daga wurin da ake tsare da su, ya kuma fice daga Najeriya.
– BBC Hausa