Gwamnatin Najeriya ta kammala shirin fidda Naira biliyan 35 dan bada rance karatu ga dalibai 7,000

0 152

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewar, gwamnatin kasar ta kammala shirin fidda kudin da suka kai naira biliyan 35, dan bada rance karatu ga dalibai dubu 70, da ke karatu a  manyan makarantu mallakarta, da suka cika dukkanin ka’idojin neman rance.

A wani rahoto da jaridar Premium Times ta fitar, ya nuna cewa an zabo daliban ne daga cikin dubu 120 da ke karatu a manyan makarantu mallakin gwamnatin kasar, da suka mika bukatar neman rancen.

Duk da dai kakakin hukumar bada lamunin karatu ta kasar Nasir Ayitogo, bai ce komai game da wannan batu da wasu majiyoyi masu tushe daga hukumar suka tabbatarwa da jaridar ba, amma ya ce suna aiki tukuru don ganin daliban sun ci gajiyar wannan shiri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samar.

Majiyoyin sun ce ba daliban za a damka wa kudin rancen karatu a hannunsa ba, tsarin da aka tanada shi ne gwamnati za ta biya kudi ne kai tsaye a asusun ajiyar makarantun, ciki kuwa harda duk wasu kudade da ake bukatar dalibi ya biya.

Haka nan, a karkashin tsarin, gwamnatin Najeriya za ta rinka baiwa kowa ne dalibi daga cikin dubu 70 din nan naira dubu 20 a duk wata, wanda zai rinka amfani da shi wajen kula da kansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: