Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin da zai yi nazarin tasirin ƙarin harain baya-bayan nan da Amurka ta yi wa kayayyakin ƙasar da ake shigarwa Amurka.
Gidan Talbijin na Channels ya ambato kakakin ma’aikatar harkokin yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Manga na bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Manga ya ce an ɗauki matakin ne bayan taron tawagar lura da tattalin arzikin ƙasar, ƙarƙashin jagorancin ministan kudin ƙasar, Wale Edun.
Yayin da sabon harajin Amurkan bai shafi man fetur – babban abin da Najeriya ta dogara da shi wajen fitarwa ƙetare – ba, matakin ya zo ne a daidai lokacin da farashin man fetur ke sauka a kasuwar duniya.
Masana dai na nuna damuwa kan yiwuwar samun cikas ko giɓi a kuɗin shiga da ma kasafin kudin ƙasar.