Gwamnatin Najeriya ta amince ta miƙa DCP Abba Kyari ga kasar Amurka bisa aikata zamba

0 311

Gwamnatin Najeriya ta amince da buƙatar Amurka ta miƙa mata ɗan sanda DCP Abba Kyari wanda ake zargi da hannu wajen aikata zambar fiye da dala miliyan ɗaya ta intanet tare da Ramon Abass.

Ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan ranar Alhamis bayan ministan ya gabatar wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja buƙatar miƙa ɗan sandan wanda tuni aka dakatar da shi don neman amincewarta.

Antoni janar ɗin ya ce ya nemi a kai Abba Kyari Amurka ne bayan buƙatar da ƙasar ta gabatar masa, inda ya yi amfani da dokar miƙa wanda ake zargi da laifi ƙasashen ƙetare ta Extradition Act a gaban kotun.

Sai dai babu ƙarin bayani a yanzu game da abin da zai faru da sauran zarge-zargen da hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi, NDLEA, take yi masa na safarar hodar ibilis idan aka kai shi Amurka.

Tun a 2021 ne Amurka ta zargi DCP Kyari da mu’amala da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi wanda kuma tuni yake tsare a ƙasar, da damfarar wasu kamfanoni fiye da dala miliyan ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: