Gwamnatin Najeriya na kokarin samar da isasshiyar wutar lantarki ga kamfanoni masu zaman kan su

0 245

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa masu zuba hannun jari kokarin da gwamnatin sa ke yi na basu isasshiyar wutar lantarki musamman a kamfanoni masu zaman kan su.

Shugaban Tinubu, yace akwai bukatar masu zuba hannun jari na kasashen waje sun samu wutar lantarki wadatacciya domin su gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yace akwai bukatar masana’antu su samu wutar lantarki, duk da ya lura cewa wasu kasashe da Najeriya ke basu wutar lantarki basa biya.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin tarayya ta hanyar kamfanin samar da wutar lantarki na Neja Delta, na kokarin ganin an tabbatar wasu masana’antu sun amfana da wutar lantarki da Najeriya ke samarwa. Babban manajan kamfanin samar da wutar lantarki na Neja Delta Chiedu Ugbo ya bayyana cewa an kammala aikin samar da wutar lantarki wanda zai samar da wutar lantarki mai karfin Mega Watt 4000, an kuma samar da Injinan da su rarraba wutar lantarkin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: