Gwamnatin mu ba zata baiwa yan Jigawa kunya Ba – Umar Namadi

0 634

Gwamna jihar jigawa Mallam Umar Namadi yace gwamnatinsa ba zata baiwa alummar jihar kunya ba, kasancewar sune suka bata wannan dama

Ya bada wannan tabbacin ne a wajen bikin murnar cin zaben sanatan Jigawa ta arewa maso yamma Dr Babangida Hussain Kazaure da aka gudanar a garin Kazaure

Mallam Umar Namadi ya ce gwamnatinsa tana aiki tukuru domin inganta rayuwar alummar jihar nan.

Yace gwamnatinsa ta tsara manufofi guda 12 da aka wallafa a harsuna turanci da Hausa kuma aka rabawa alummar jihar nan.

Mallam Umar Namadi ya kara da cewar gwamnatinsa zata bada fifiko ga cigaba matasa Ya kuma ce kofarsa abude take don masu bada shawara idan bukatar hakan ta taso

Leave a Reply

%d bloggers like this: