Gwamnatin jihar Kano ta koka kan karin kudin rajistar daliban da hukumomin jami’ar Bayero dake Kano, BUK suka yi ba zato ba tsammani.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Sunusi Na’Isa ya fitar jiya a Kano.
Mista Na’Isa ya ruwaito kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Dakta Yusuf Kofarmata, yana bayyana faruwar lamarin a matsayin abin ban tsoro yayin ziyarar ban girma da ya kai wa mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Abbas a ofishinsa.
A cewar sanarwar, Kwamishinan ya bayyana cewa, makasudin ziyarar tasa ita ce karfafa dankon zumunci tsakanin gwamnati da BUK, da kuma tattaunawa kan karin kudaden rajistar ba zato ba tsammani.
Kofarmata ya bayyana cewa tuni gwamnati ta shirya daukar nauyin ‘yan asalin jihar Kano 101 domin samun digiri na biyu a jami’o’in gida da waje.
Ya kuma yi kira ga mataimakin shugaban jami’ar da ya duba yiwuwar rage kudin rijistar domin dalibai marasa galihu.
Da yake mayar da martani, mataimakin shugaban hukumar ya yi maraba da kwamishinan tare da taya shi murnar nadin da aka yi masa, wanda ya bayyana a matsayin wanda ya cancanta.