Gwamnatin Kano ta amince da Naira 71,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi

0 35

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta daddale naira 71,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta da za ta biya ma’aikatanta.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a fadar gwamnatin jihar ranar Talata bayan ganawa da wakilan ƙungiyar ƙwadago.

Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ta ce ƙarin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2024.

Kano ta zama ɗaya daga cikin jihohin da suka amince da biyan sama da abin da gwamnatin tarayya ta amince na N70,000 tun a watan Yuli.

Jihohin Legas da Rivers ne kan gaba bayan sun amince da N85,000, sai kuma Neja da ta ce za ta biya N80,000.

Leave a Reply

%d bloggers like this: