Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce, ta karbi manyan motocin yaki na musamman guda biyu da kuma karin ‘yan sanda mutum 200 da suka samu horo na musamman a rundunar ‘yan sandan kasa inda aka turo su jihar.
Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna jiya Lahadi.
Yace wannan wani shiri ne don a karfafa yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran nau’ikan laifuka.
A ziyararsa ta karshe a jihar Kaduna, I-G ya yi alkawarin tura kayan aiki da ma’aikata domin karfafa yaki da nuna irin kwazon rundunar ‘yan sandan kasa a jihar Kaduna.
Da yake jawabi ga jami’an gwamnan Uba Sani ya bayyana jin dadin sa da kubutar da sama da dalibai 137 na makarantar Kuriga da aka sace, yana mai cewa sakin nasu wani kokari ne a wani atisayen dakarun hadin guiwa. Yace za’a tura jami’an kananan hakumomi da kauyukan Chikun, Kajuru, Birnin-Gwari da sauran guraren da ake fuskantar tashe-tashen hankula a jihar.