Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahotannin yin garkuwa da mutane da dama a wani wuri mai tazarar kilomita kadan daga Kagarko kan hanyar Kaduna Abuja.
Da yake karyata rahotannin sace-sacen da aka wallafa a wata jarida da safiyar Juma’a, kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan a wata sanarwa da ya fitar ya ce rahoton yaudara ne, ba gaskiya ba ne kuma ba shi da tushe.
Ya ce sabanin rahoton, bayanan da aka samu daga hukumomin tsaro da karamar hukumar Kagarko sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi kauyen Gwaje na hanyar Kagarko zuwa Jere a ranar Laraba 5 ga Afrilu 2023 suka yi awon gaba da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba daga cikin motoci biyu.
Daga baya aka gano motocin babu kowa.
Ya ce lamarin bai faru a Iche ba kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito, ya kara da cewa bayanin garin Kagarko na kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ba daidai ba ne.
Aruwan ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda rahotannin da ake yadawa na yaudara da rashin alheri suka samu karbuwa a shafukan sada zumunta da sauran su.
- Comments
- Facebook Comments