Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana duba yiwuwar dawo da Yansakai wanda ta rushe su a baya

0 224

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana duba yiwuwar dawo da Yansakai wanda ta rushe su a baya, domin tallafawa Jami’an tsaro a yakin da suke na yan bindigar a Jihar.

Shugaban Kwamatin Tsaro da kuma Gurfanar da Yan bindiga a Jihar Zamfara Dr Abdullahi Shinkafi, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a birnin Gusau.

Dr Shinkafi, wanda shine Mai bawa Gwamnan Jihar Zamfara Shawara kan Lamuran da suka shafi Gwamnati, ya ce dawo da Yansakai zai taimakawa hukumomin tsaro wanda suke cigaba da fito da yan bindiga daga Maboyarsu da kuma masu taimaka musu.

Haka kuma ya ce matakin gwamnatin tarayya na dakatar da hanyoyin sadarwa a jihar ta Zamfara, da kuma wasu yunkuri da gwamnatin Jihar dake yi domin dakile hare-haren yan bindiga ya fara samar da kyakkyawan sakamako.

Kazalika, ya bukaci mutane su kasance masu tallafawa kokarin gwamnati na dawo da zaman lafiya a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: