Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890

0 40

Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.225 ga dalibai 890 da ke karatu a makarantar Tulip International College (NTIC), Mamudo.

Za a cigaba da biyan wannan tallafi har tsawon shekaru shida, tun daga matakin karamar sakandire har zuwa ajin karshe na babbar sanadire.

A yayin bikin kaddamar da bayar da tallafin a dakin taro na NTIC Mamudo, Gwamna Mai Mala Buni, wanda Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na Jiha, Alhaji Tonga Betara, ya wakilta, ya jaddada aniyar gwamnati na karfafa bangaren ilimi da gina tubali mai karfi don amfanin ƙarni masu zuwa.

Ya bayyana cewa wannan shirin tallafin yana cikin matakan da gwamnati ke dauka don farfado da ilimi a jihar. Gwamnan ya bukaci daliban da suka ci gajiyar tallafin da su kasance masu da’a, su dage da karatu, kuma su nuna himma wajen cimma nasara.

Gwamna Buni ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta ware Naira miliyan 2.5 ga kowane dalibi a duk shekara.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ilimi na Firamare da Sakandare, Assoc. Prof. Abba Idriss Adam, ya bayyana shirin a matsayin wani babban jari a bangaren ilimi da zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta al’umma a nan gaba.

Leave a Reply