Gwamnatin jihar Nasarawa ta dakatar da duk wata Ƙungiyar ’yan banga da ke aiki a faɗin ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma haramta duk wata ƙungiya, ko rukunin al’umma da ke da alaƙa da ƙungiyar da ke gudanar da ayyukanta a ƙarƙashin ’yan banga na ƙabila.
Hakan na zuwa ne bayan taron gaggawa kan harkar tsaro da Gwamna Abdullahi Sule ya kira. Gwamnatin jihar ta kuma ba da wa’adin makonni biyu ga ɗaukacin ƙungiyoyin ’yan bangan su miƙa kakinsu da makamansu ga Kwamishinan ’yan sandan jihar, Shehu Nadada.