Gwamnatin jihar Katsina ta dauki malaman makarantun Firamare da sakandire 7,326

0 337

Gwamnan jihar katsina Dikko Radda, yace gwamnatin sa ta dauki malaman makaranta 7,326 a makarantu Firamare da sakandire na jihar a kokarin na inganta tsarin koyarwa a jihar.

Gwamnan tace ta hanyar tantancewa aka dauki malaman makarantar wanda hakan yayi dai-dai da adadin da bankin duniya ke bukata.

Ya kumma jadadda kudirin sa na kawo karshen shigar da harkokin siyasa a bangarang koyarwa. Ya yi ikirarin cewa daukar ma’aikata a lokutan baya ana yin su akai-akai ba tare da la’akari da cancantar mai nema ba, yana mai tabbatar da cewa a halin yanzu za’a na daukar ma’aikata ne bisa cancanta

Leave a Reply

%d bloggers like this: