Gwamnatin jihar Katsina ta amince da biyan ₦640.6M a matsayin tallafin kudin karatu ga dalibai

0 292

Gwamnatin jihar Katsina ta amiince da sakin kudi kimanin Naira Milyan 640.6 domin biyan tallafin kudin karatu ga dalibai ‘Yan asalin jihar dake karatu a manyan makarantu na gaba da sakandire.

Gwamnatin jihar tace dalibai kimanin 14,443 na Zangon karatun shekarar 2020/2021, da kuma wasu daliabai 33,492 dake karatu a tsakanin shekarar 2021/2022 a manyan makarantun gaba da sakandire 126 tuni suka samu nasu kudin tallafin karatun.

Daraktan walwala na hukumar bada tallafin karatu na Jihar Sirajo Umar shine ya sanar da haka a jiya laraba lokacin da yake yiwa kwamitin gudanarwa karin bayani.

Ya kuma kara da cewa hukumar bada tallafin karatu ta jihar zata biya kudin Alawus-alawus ga daliban domin rage radadin tsadar rayuwa da ake ciki.

A cewar sa, gwamnatin jihar zata samar da damar-makin tallafin karatu a mataki na kasa da kasashen ketare domin karfafawa dalibai gwiwar neman ilimi.

Umar sarajo, yace gwamnatin jihar zata hada akai da kungiyoyin samar da cigaba domin tallafawa daliban wajen yin karatu, ta hanyar samar da tsare-tsare masu kyau a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: