Gwamnatin jihar Kano za ta biya ma’aikatan jihar albashin watan Marsi kafin bikin karamar Sallah

0 93

Gwamnatin jihar Kano ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin cewa za a biya su albashin watan Marsi kafin bikin karamar Sallah da ake sa ran za a fara biya daga ranar 25 ga watan nan.

Sakataren gwamnatin jihar, Faruk Ibrahim, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano jiya Litinin.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, an shirya taron manema labarai ne domin yiwa jama’a bayani kan kokarin da gwamnatin jihar ke yi na kaucewa sabani da aka samu a lokacin biyan albashin watan Fabrairu.

Da yake jawabi, Mista Ibrahim ya ce gwamnati na sane da shirin bikin Eid-el-Fitr dake gabatowa, kuma za ta tabbatar da biyan albashin watan Maris kafin bukukuwan.

A cewarsa, ma’aikatan gwamnati a jihar za su tantance albashinsu na watan Maris kafin a biya su, domin kiyaye duk wani sabani a cikin aikin kamar yadda aka rubuta a baya.

Mista Ibrahim ya ce matakin ya biyo bayan korafe-korafen da ma’aikata ke yi na rashin daidaito da suka hada da cire musu albashin watan Janairu da Fabrairu.

Leave a Reply