Gwamnatin jihar Kano ta shigar da ƙara ta zamba da take zargin Abdullahi Ganduje

0 238

Gwamnatin Jihar Kano ta shigar da wata sabuwar ƙara ta zamba da ake zargin tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Ganduje, Kwamishinansa na ƙananan hukumomi, Murtala Garo, da wasu mutum biyu, Lamin Sani da Muhammad Takai. Sabbin tuhume-tuhumen sun haɗa da haɗin baki wajen aikata laifi, da cin amanar jama’a, da bayar da bayanan ƙarya, da kuma almundahana.

Ana tuhumar su da zargin karkatar da Naira biliyan ₦57.4 daga kuɗaɗen tallafin da ake bai wa ƙananan hukumomi 44, da ake zargin an zuba kuɗaɗen cikin asusun ajiyar kuɗi na kashin kai da na kamfanoni daban-daban.

Gwamnatin jihar ta kuma zargi waɗanda ake tuhuma da canza kuɗaɗen zuwa daloli don amfanin kansu, inda ake zargin an yi amfani da kuɗaɗen wajen sayen kadarorin da suka haɗa da wurin zama na musamman a kan titin Murtala Muhammad a Kano, wani fili na kasuwanci a Dubai, wani Otal mai darajar biliyoyin Naira a Abuja, da gidajen mai da dama a Kano.

Kundin ƙarar ya nuna cewa jihar tana shirin kirawo shaidu 143 a cikin shari’ar.

Ba a tsayar da ranar shari’a ba tukuna kawo yanzu. Wannan sabon ci gaban na zuwa ne bayan jerin matakan shari’a da Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauka kan Ganduje da abokan aikinsa, ciki har da wata ƙara da aka shigar a ranar 4 ga Afrilu da kuma wasu ƙarin tuhume-tuhume da aka ƙara shigar wa a ranar 16 ga Yuli, inda ake zargin Ganduje da tsohon Kwamishinan Shari’a, Musa Lawan, da haɗin baki wajen aikata laifi da almundahana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: