Zulkiflu Abdullahi Dagu
Gwamnatin jihar Jigawa zata samar da Karin makarantun islamiyyu guda 150 domin karantar da Fulani makiyaya
Sakatariyar gudanarwa ta hukumar llmin Ya’Yan Fulani makiyaya ta jihar Jigawa Hajia Ramatu Muhammad ta sanar da hakan ga manema labarai a ofishinta
Tace a yanzu haka akwai irin wadannan cibiyoyi 400 a sassan jihar nan da ake koyar da Fulani yadda ake alwala da karanta Alqurani mai girma da kuma yadda ake Sallah.
Hajia Ramatu Muhammad tana mai cewar babbar matsalar da suke fuskanta ita ce rashin makarantar kwana ta Fulani makiyaya, inda ta roki gwamnatin jiha data samar da makarantar kwana ta Fulani makiyaya domin basu damar cigaba da karatu bayan kammala firamare.
Ta kara da cewar hukumar ta samu nasarori masu yawa wajen gina Karin ajujuwan karatu da sayen kayayyakin makaranta ga dalibai da kuma sayen kayayyakin koyo da koyarwa ga makarantun yayan Fulani makiyaya. Hajia Ramatu Muhammad tacigaba da cewar gwamnati ta kammala shirye shiryen bude ajujuwan koyar da fasahar sadarwa ta zamani a karamar sikandare Fulani makiyaya dake Dangan Tsaure da nufin koyar da Fulani makiyaya yadda ake sarrafa naurar komputa.