Gwamnatin Jihar Jigawa zata cigaba da gudanar da manufarta ta bada ayyuka a mazabun ‘yan majalisar dokokin jiha guda 30 kasancewar ayyukan na taba rayuwar mutanen karkara kai tsaye.
Kwamishinan albarkatun ruwa na jiha Ibrahim Garba Hannun Giwa, wanda daraktan tsare-tsare na ma’aikatar Kabiru Inuwa Sankara ya wakilta ya bayar da tabbacin a yau, yayin bude tayin bayar da ayyukan kwangilar ruwan sha a mazabun ‘yan majalisa 15 a harabar ma’aikatar.
A nasa jawabin mukaddashin manajan daraktan hukumar samar da ruwan sha a matsakaitan garuruwa, Injiniya Adamu Garba ya ce ayyukan sun hadar da samar da sabbin tashoshin ruwa 45 masu aiki da hasken rana da gyare-gyaren gidajen ruwa 20 da sanya na’urar somo da killace gidajen ruwa a mazabu 15 na ‘yan majalisar dokokin jihar.
Ya ce ayyukan wanda za’a yi akan kudi sama da miliyan 400 kuma kamfanoni 153 ne suka nemi bukatar gudanar da ayyukan wadanda daga ciki za’a tantance 51, inda ya yi kira ga kamfanonin da zasu yi nasara su tabbatar sun gudanar da aikin mai ingancin kuma akan lokaci.