Gwamnatin jihar Jigawa tana duba yiwuwar samar da kananan madatsun ruwa guda goma a jihar

0 161

Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin ambaliyar ruwa da kuma sauyin yanayi Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya sanar da hakanta cikin shirin Radio Jigawa mai suna Jigawa A Yau.

Ya ce za a yi hakan ne domin bunkasa noman rani da kuma tattalin arzikin alummar jihar nan.

Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya kuma ce gwamnati tana tunanin samar da kananan madatsun ruwan ne a wuraren da Kogi ya ratsa domin dakile matsalar ambaliyar ruwa da kuma kwararan ruwan kogi zuwa gonaki.

A cewarsa ana gudanar da bincike domin gano wuraren da ya da kamata a samar da kananan madatsun ruwan a jihar nan, inda ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin sake duba madatsun ruwa na kasar nan domin gyara su.

Ya ce a bara gwamnatin jiha ta samu gagarumar nasarar wajen dakile matsalar ambaliyar ruwa ta hanyar yin aiyukan jinga da kuma kandagarken wuraren da ruwan kogi ke kwarara.

Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya kara da cewar tuni gwamnatin jiha da kwararru suka fara aikin jinga a wasu muhimman wurare domin dakile ambaliyar ruwa a bana.

Leave a Reply