Gwamnatin jihar Jigawa tace zata raba gidajen sauro da suka kai miliyan 3 da dubu 200

0 199

Gwamnatin jihar Jigawa tace zata raba gidajen sauro da suka kai miliyan 3 da dubu 200 nan da makonni 2 a wani yunkuri na magance matsalar cutar maleriya a tsakanin jama’a.

Kwamashinan lafiya Dr. Abdullahi Muhammad Kainuwa ya bayyana haka lokacin bikin kaddamar ada rabon dagaje masu dauke da maganin sauro wanda gidauniyar  D-BAFS ta samar ga kwalejin sakandiren kere-kere ta Hadejia.

Da yake samun wakilcin daraktan sashen kula da magunguna na ma’aiakatar ya yabawa gidauniyar bisa karamcin, wanda yace yana daga cikin manufofin gwamnatin Umar Namadi 12.

Yace gwamnatin jihar jigawa tana bakin kokari wajen magance matsalar zazzabin cizon rauro.

A cewar kwamashinan, za’ayi rabon ne ga mata masu shayarwa da kananan yara yan kasa da shekaru 5 da kuma cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.

Da yake jawabi tun da farko shugaban gidauniyar Mr. Jean Mac Ricca yace, sun zabi makarantar ne domin raba gidajen sauro 800 ga daliban domin tallafawa gwamnatin jiha a yunkurin ta na yaki da cutar cizon sauro, yana mai cewa za’a karbi tsaffin gidajen sauron domin sake sabunta su.

A jawabansu wakilin kwamishinan ilimin manyan makarantu da muhalli da sauran daraktocin ma’aiakatu sun yabawa gidauniyar D-BAFS ta kasar Jamus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: