Gwamnatin jihar Jigawa ta tura tawagar kwararru zuwa jihar Edo domin kwaikwayo tsarin koyo da koyarwa

0 237

Gwamnatocin jihohin Jigawa da Delta sun tura tawagar kwararru zuwa jihar Edo domin kwaikwayo tsarin koyo da koyarwa da inganta fannin ilimi a matakin farko a jihohinsu.

Ziyarar ta gwamna Umar Namadi da takwaransa na jihar Delta Shariff Oborevwori, sun samu wakilcin baban sakatare ilimi matakin farko na jihar Jigawa Sagir Muhammad Sani da kuma Dr. Ashobogwu Nze Kingsley kwamishinan ilimin jihar Delta.

Wakilan gwamnonin Biyu sun ziyarci gurare da dama a jihar ta Edo domin kwaikwayon tsarin ilimin jihar.

Haka kuma wakilan sun samu tarba daga shugaban hakumar ilimi matakin farko ta jihar da kuma Shirin NewsGlobe domin kulla alakar hulda da juna. Sun tattauna muhimman batutuwa da dama wanda ake sa ran zasu gabatar dasu ga gwamnoninsu domin aitawatar dasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: