Wannan dai na karashin wani tsari na kiwon dabobi na Gwamnatin jihawa, wanda ke da manufar bunkasa tattalin arzikin mata da iyalai a cewar Kamfanin dillancin labarai.
Mukaddashin shugaban majalisar karamar hakumar Birniwa ya raba awakin 264 ga mata 88 a fadin yankin domin bunkasa walwalar mata a yankin.
Jami’in yada labaran yankin yayi bayanin cewa kwamashinan aikin gona da albakatun na jiha Muttaka Namadi ne ya wakilci gwamna Umar Namadi a wajen bikin rabon tallafin.
Gwamnan jihar Jigawa yace gwamnatinsa ta gudanar da ayyukan bayar da jari da dama da nufin tallafawa matasa da mata a fadin jiha.