Gwamnatin Jihar Jigawa ta miƙa Dajin Baturiya ga Hukumar Kula da Gandun Daji ta Ƙasa

0 191

Gwamnatin Jihar Jigawa ta miƙa Dajin Baturiya wato Hadejia Wetland Game Reserve ga Hukumar Kula da Gandun Daji ta Ƙasa (National Park Service).

A watan Yuli ne, Gwamnan jihar Mallam Umar Namadi ya karɓi baƙuncin shugabannin hukumar domin fara shirin miƙa dajin ga gwamnatin tarayyar.

Dajin Baturiya ya haɗa ƙananan hukumomi uku, wato Auyo, Kirkikasamma, da  kuma Guri, kuma yana da muhimmanci ga tattalin arziƙi, muhalli, da yawon buɗe ido.

Shirin miƙa dajin ya fara ne tun shekarar 2011, amma an kammala shi a shekarar 2022 lokacin da aka sanya hannu kan takardar amincewa da miƙa dajin Baturiya da sauran dazuka guda goma a kasar.

Ministan Muhalli ya bayyana cewa dazuka irin su Baturiya suna da matuƙar muhimmanci, kuma za a yi amfani da fasahar zamani wajen kula da su.

An kuma haɗa hannu da Bankin Duniya ta shirin ACReSAL domin samar da kayan aiki da horar da ma’aikatan da zasu kula da dajin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: