Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe kudi fiye da naira miliyan dubu 1438 wajen sayen kayayyakin rage radadin cutar corona
Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe kudi fiye da naira miliyan dubu daya da miliyan 438 wajen sayen kayayyakin rage radadin cutar corona da kuma bayar da kwangila ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa a jihar nan a shekarar da ta gabata.
Wakilin ma’aikatar kudi ta jiha Alhaji Haruna Danlami ya bayyana hakan a kasidar da ya gabatar a taron fadakar da kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa hanyoyin samun kwangila a saukake domin rage karayar tattalin arziki da annobar corona ta haifar, wanda gwamnatin jiha ta shirya a Maimuna Millenium Park, Hadejia
Yace akasarin ma’aikatu da hukumomin gwamnati na da rarar kudade da zasu aiwatar da kashi na biyu na shirin gwamnati na tallafawa kananan ‘yan kasuwa da bayar da kananan kwangiloli.
A jawabinsa, kwamishinan ilmi, kimiyya da fasaha na jiha, Dr Lawan Yunusa Danzomo, yace ma’aikatarsa zata baiwa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa guda 200 kwangiolin sayowa da samar da kayayyakin koyo da koyarwa, nan da karshen wannan shekara.