Jigawa ta kafa wani kwamiti domin magance ambaliyar ruwa

0 151

Gwamnatin jihar jigawa ta kaddamar da wani kwamati mai wakilai tara domin shawo kan matsalar ambaliyar ruwa.

Da yake kaddamar da kwamatin, sakataren gwamnatin jiha Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini, ya bukaci yan kwamatin da su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da adalci, inda ya ce an zabe su ne sakamakon kwarewar da suke da ita a fannoni daban-daban.

Yace kwamatin zai taimakawa gwamnati wajen magance matsalolin ambaliyar ruwa, da jihar Jigawa take fama da shi duk shekara, ta hanyar bayyana wuraren da iftila’in yafi shafa da hasarar da hakan ke haifarwa da kuma baiwa gwamnati shawarwarin da suka dace domin shawo kan matsalar. Ya sanar da cewa kwamitin yana karkashin shugabancin mai baiwa gwamna shawara kan shigar da al’umma da kuma kungiyoyin cikin harkokin gwamnati, Alhaji Hamza Muhammad Hadejia, da daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a ma’aikatar mullahi, Mallam Bello Idris, a matsayin sakataren kwamitin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: